Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Ƙasar Saudiyya Ta Nemi Afuwa Bisa Zaluntar Alhazan Nijeriya (Karanta)

0 7

Image may contain: 2 people, people sitting and indoor

Gwamnatin ƙasar Saudi Arabia ta nemi gafarar Nijeriya bisa zaluntar wasu alhazan jihar Nassarawa guda biyu da jami’an kwastam su ka yi a filin jiragen sama na Prince Muhammad Bn Abdulaziz da ke Madinah a ranar Laraba.

Jami’an kwastam din Saudi Arabia dai sun suburbudi Audu Muhammad da Ibrahim Godi ne jim kadan bayan isarsu daga Abuja.

Sakataren hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) Bello Tambuwal ya ce jami’an kwastan din sun nemi kebewa da alhazan biyu ne bayan kammala yi musu duk wani bincike da ake yi a filin jiragen saman. “Hakan ce ta sa alhazan su ka ji tsoro su ka ki bada hadin kai, nan take kuwa jami’an su ka yi musu rubdugu.”

Bello Tambuwal ya ce daga bisani mahukuntan Saudi Arabia sun bada hakuri kuma sun dauki nauyin jinyar alhazan bayan da su ka kai su asibiti.

Mataimakin gwamnan jihar Madinah, Wahid Asahin da mataimakin ministan aikin Hajji Muhammad Abdulrahman Al Bijawi ne su ka ziyarci mahajjatan a dakinsu da ke otal din Riyad Al Zahra da ke unguwar Markaziyya bayan da aka sallamo su daga asibitin.

Wahid Asahin ya bayyana takaicinsa game da faruwar lamarin tare da tababatarwa da jami’an alhazan Nigeria cewa hakan ba zata sake faruwa ba, kuma tuni aka dauki matakan ladabtarwa akan jami’an kwastan din da suka suburbudi alhazan.

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.