Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Allah Yayiwa Tsohon Dan Wasan Hausa Kasimu Yero Rasuwa

0 11

Marigayi Kasimu Yero

An yi jana’izar tsohon shahararren dan wasan kwaikwayon Hausa, Kasimu Yero wanda ya rasu a Kaduna ranar Lahadi, kamar babban dan marigayin ya shaida wa BBC.

Marigayin wanda ya rasu yana da shekara 70 ya yi doguwar jinya ne, kamar yadda dansa Mansur Kasimu Yero ya ce.

Alhaji Kasimu Yero ya yi fice ne a shekarun 1980 lokacin da yake fitowa a shirye -shiryen kafar yada labarai ta kasar wato NTA – a wasannin Magana Jari Ce (na Hausa da na Turanci) da Karanbana da dai sauransu.

Ana ci gaba da mika sakon ta’aziyya game da rasuwar dan wasan wanda ya shahara wajen barkwanci.

Jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya yi fatan Allah Ya jikan marigayin, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Marigayin ya bar ‘ya’ya takwas da kuma jikoki 10.

Wadansu masu ta'aziyya a kofar gidan marigayin da ke unguwar Magajin Gari Kaduna

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.