Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

An Yayyafawa Masana’antar Shirya Fina Finai Wato Kannywood Ruwa (Karanta Kaji)

0 12

KWAMITIN KULA DA GIDAJEN KALLO DA SINIMOMI

Sharfuddeen Baba, Kano.

Masana’antar Kannywood ta kasance masana’anta wadda ta fi kowacce a Arewacin Najeriya samar da ayyukan yi ga matasa cikin ƙanƙanin lokaci, amma kasuwanci a cikinta ya gurgunce tsawon shekaru sakamakon dogaro da hanya ɗaya ta samar da kuɗaɗen shiga (wato kasuwannin siyar da CD/DVD). A lokuta da dama mutane da dama sun yi yunkurin kawo canji a tsarin kasuwanci amma abin ya ci tura. Da alama a wannan karon haƙa zai cimma ruwa. Dalili kuwa shi ne, kamfanin shirya fina-finai na MOTION PICTURE PRODUCTIONS LTD tare da hadin gwiwar CERTIS NIGERIA LTD, sun zaburo da sabon tunani wanda zai tafi tare da zamani wajen ganin cewa an farfaɗo da harkar kasuwancin fina-finai ta yadda kowa zai ci moriyar abin, kama daga Gidajen Kallo, Masu shirya fina-finai, ƙungiyoyin ƴan fim har ma da gwamnati.

Kannywood Box Office, zai kasance sabon dandamali a daidai lokacin da harkar tattalin arzikin masana’antar shirya fina-finai ta tabarbare, kuma satar fasaha ta kai tsaiko yadda masu saka jari cikin harkar ke guduwa kuma fasaha ke dakushewa. Hanya ɗaya tilo da za’a fito daga cikin wannan duhu shi ne ta hanyar farfaɗo da Sinimomi. Kiyasi na baya bayan nan na nuna cewa a Jihar Kano kawai, akwai kimanin kananan sinimomi 8,000, wadanda ta hanyar amfani da tsari da fasahar zamani za’a iya cin cikakkiyar moriyar su, wadda zata kawo ɗinbin arziki ga masana’anatar. Wannan tunani ya sa shugabannin waɗancan kamfanunuwa guda biyu suka yunƙura wajen fara samar da wata na’ura, wadda su ka kira da YODA. Ita wannan na’ura ta majigi (projector) an tsara ta yadda sai da kati mai ajiyar fasaha kawai za ta iya amfani da ita (memory card) kuma ba wani mai irinta a faɗin duniya sai kamfanin CERTIS. Ta wannan hanya za’a tsare duk wani fim da aka saki daga ɓarayin fasaha, domin ko ka sami wannan kati ka saka a wata komfuta ba zai yi amfani ba sai a na’urar YODA. Dandamanlin zai kasance waliyyin ɗaura aure tsakanin gidajen kallo da masu shirya fina-finai ta hanyar haɗa yarjejeniya yadda kamfunan za su karɓi fina-finai daga hannun masu shiryawa su riƙa nunawa a gidajen kallo ta hanyar wannan na’ura ta YODA.

An sami gidajen kallo kimanin 200 da za’a fara gwaji da su a karshen watan Yuni na shekarar 2017 kuma a ƙididdigar da su ka yi ya nuna cewa aƙalla a rana guda kowanne gidan kallo zai iya samun N7000, wato kaso 47% cikin ɗari na kuɗaɗen da za’a samu, yayin da masu fim za su iya samun N4000 wato kaso 27% a gidan kallo guda, inda masu shirya tsarin da kula da shi za su sami N2000 wato kaso 14%, sai hukumar fina-finai wadda za’a riƙa cire wa harajin N1400 wato kaso 9.8% (maimakon kusan kaso 10-38% da gwamnati za ta iya karɓa kai tsaye). Dandamalin ya fitar da tsarin bawa fina-finai aji kama daga A, B da C, wanda kuɗin da mai shiryawa zai samu ya danganta da ajin fim ɗinsa, hikimar itace samar da inganci wajen irin fina-finai da za’a riƙa fitarwa. A shekara guda, wanda ya yi fim mai inganci zai iya tashi da kimanin Naira miliyon N42,000,000. Haƙiƙa wannan tsari zai zama wani juyin-juya-hali a wannan masana’anta domin a halin da ake ciki babu wani fim da zai iya wuce sati biyu a kasuwa, kuma ribar da za’a samu ba ta taka-kara-ta karya ba.

Wannan sabon tsari zai samar da hanyar kuɗin shiga kai tsaye ga masu gidajen kallo, da masu shirya fim har ma da gwamnati, ya kuma samar da sabuwar hanya da ake kishirwarta a wannan lokaci da kasuwar fim ta kusa rugujewa. Sannan gagara-badau shi ne yaƙar masu satar fasaha waɗanda a yanzu ke lashe kusan kashi 90% na gumin masu shirya fim, domin wannan na’ura ita kaɗai ce tilo, kuma ta sami sahalewar British Council da Alu ja cikin jami’o’in fasaha a duniya wato Massachusetts Institute of Technology (MIT). Sannan za’a bawa ƙungiyoyi damar samun bayanai da kuma cuɗanya da sauran masu ruwa da tsaki yadda za’a iya samun cikakken tsari da kowa zai amfana daga gare shi.

A yau, masana’anatar Kannywood ta dogara da siyar da DVD, wanda idan tsarin da aka zo da shi ya yi tasiri DVD zai kasance a mataki na 4 bayan matakan Sinimomi da gidajen kallo, gidajen talabijin da na’urar sadarwa (Online irinsu Netflix, IrokoTV da sauransu) sannan ne za’a fara maganar DVD, wanda a ƙa’ida lokacin da fim ya kai ga DVD, kamata ya yi a ce mai shirya fim ɗin ya gama mayar da kudinsa har ya fara samun riba, yadda DVD zai kasance ribar kafa.

A ƙarshe muna ganin cewa farawa da tsarin sinimomi da gidan kallo zai kasance ɗan ba na ganin cewa duk waɗannan tsaruka sun zama zahiri, yadda wannan masana’anta da ke da ɗimbin arzikin da ba’a tatsa ta farfaɗo daga cikin mawuyacin halin dakushewar kasuwancinta zuwa ga matakin arziki da faɗaɗa izuwa ga sauran jihohin Nigeria da Afurka har ma da duniya.

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.