Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Bikin Sallah: Manyan Jaruman Kannywood Zasu Ketare Najeriya Domin Gudanar Da Wasanni

0 11

Wasu manyan jaruman kamfanin shirya fina-finan Hausa na Kannywood ba za su yi shagulgulan bikin karamar Sallah a gida Najeriya ba, inda suka shirya yin wasanni a kasashe masu makwabtaka da kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa Adam A. Zango ya shirya tsaf domin tafiya jamhuriyar Nijer inda zai kayatar da masoyansa da ke can a lokacin bikin Sallah.

Bikin Sallah: Manyan jaruman Kannywood za su ketara Najeriya domin gudanar da wasanni

A daya bangaren kuwa kasar Ghana kuwa za ta samu bakuncin Jamila Nagudu, Halima Atete da Zaharadeen Sani.

Zaharaddeen ya bayyana cewa za su amsa gayyata ne daga dumbin masoyansu da ke can, wadanda suka bukaci su zo su nishadantar da su a lokacin bikin sallar.

Ya kara da cewa mutanen Ghana su na matukar kaunar shirye shiryen Kannywood kuma wannan ita ce damar su nuna masu cewa suna tare da su.

Za su bar Najeriya a yau Juma’a, kuma kowannen su zai yi wasanni a gurare daban daban.

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.