Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Cika Alkawari Yayi A Karanci A Masana’antar Kannywood – Inji Wani Jarumi

0 10

Image result for kannywoodSani Sale Yareema Jarumi, Mawaƙi, furodusa sannan kuma kwararren ta fuskar tsara wuraren taron bukukuwa, hotuna da sauransu. Kana kuma shi ne shugaban Kamfanin Yareema Production, a tattaunawar sa da Kannywoodtoday Jarumin wadda ake kallo amatsayin sabuwar fuska, gogaggen ma’aikacin Banki a baya, ya yiwa Kannywoodtoday bayanin yadda ya tsinci kansa a wannan harka ta fina-finan Hausa, sannan kuma ya yi tsokaci kan yadda yake kallo masana’antar Kannywood, Jarumi Yareema ya bayyana aniyarsa ta gudanar da harkokin finfinai cikin tsari da kuma duban gaba kuma aduba baya.
Ga yadda tattaunawar ta kasance.

Kannywoodtoday: Za muso jin wanda muke tare dashi?

Yareema: Alhamdulillahi sunana Sani Sale Yareema shugaban Kamfanin Yareema Production wanda aka fi sani da Yareema Gani a fili, haifaffen Garin Kano.

Kannywoodtoday: Kasancewarka Jarumi, Producer, Mawaƙi sannan kuma kwarrare ta fuskar tsara wuraren taruka, shin ko ya Yareema ya tsinci kansa cikin waɗannan muhimman abubuwa har guda huɗu alokaci guda?

Yareema: Kamar yadda ka sani kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa musamman idan aka samu jajircewa kan abinda mutum yake so ya yi, karka manta cikin tarihina kamar yadda aka sani ni ma’aikacin Banki ne shi ne aikina na ƙarshe wanda daga nan na tsunduma cikin wannan sana’a. Don haka duk abinda kake so ba zai baka wata wahala ba, soyayyar abinda nake so ne yasa har kaga na haɗa abubuwa huɗu ina yi alokacin guda, da sauran waɗansu da sai tafiya tayi nisa zaka sansu. Saboda haka ganin abubuwan da ake gudanarwa a masana’antar shirya fina-finan Hausa yasa na aminta da shiga harkar domin bayar da tamu gudunmawar, da kuma kawo gyara a wurin da ya dace idan mun samu ikon hakan.


Wani bangaren kwalliya daga kamfanin Sani Yareema

Kannywoodtoday: Kasancewar akwai ɓangarori a harkar fim, zuwa yanzu ko wane matsayin Yareema ke fita a cikin fina-finan Hausa?

Yareema: Gaskiya na fito a abubuwa masu yawa domin na fito a matsayin Jarumi na fito amatsayin Alhaji na fito a muhutin alƙali da sauran abubuwa kwarai da gaske.

Kannywoodtoday: Shin waɗannan fina-finai da Yareema ya ambata ya fitowa acikinsu, shin sun shiga kasuwa ne ko har yanzu suna hanyar fitowa?

Yareema: Kwarai akwai wani fim mai suna Asibiti shi Series ne ma kuma kasan fim series an fi ganinsa a tauraron Ɗan Adam da sauransu, wannan ban sani ba ko sun sake shi zuwa yanzu, sai Kuma wani fim nawa ne ma na kamfanin na mai suna Gani A Fili, Mafiya, Sakatare Janar da Jakar Mata duk suna nan kan hanyar fitowa, sai kuma wani fim da kamfanin walwala na Mustapha JT mai suna Mai Nayi shima ban sani ba ko an sake shi. Fina-finai suna nan sun kai guda biyar suna kan hanyar fitowa insha Allah.

Kannywoodtoday: Me wannan fim na Gani A Fili ya ƙunsa ko wane saƙo ake son isarwa acikinsa?

Yareema: Watau mutane suke ta tambaya wane Gani A Fili musamman jin waƙar dana yi mai suna gani a fili, wannan tasa idan nazo wani wuri sai kaji ana cewa a’a kun ganshi a fili, sau da yawa ina cikin mota mai duhun gilashi ko na ɗan yi wani Basaja yadda ba‘a gane ni ba, wata rana na bita wani wuri sai kawai wata yarinya tace la gashi afili yau, yau munga Yareema a fili, hakan tasa na samar da wannan fim mai suna gani a fili domin nishaɗantar da jama’a da kuma faɗakarwa kwarai da gaske.

Kannywoodtoday: Kasancewa harkar fim wata sana’a ce da ake yiwa wani irin kallo, kai kuma gashi tsohon ma’aikacin Banki ne, shin ya zaka kwatanta aikin Banki da wannan sana’a fina-finan Hausa?

Yareema: Gaskiya lokacin dana shigo wannan harka na hangi matsaloli domin na fahimci akwai matsaloli kwarai da gaske, ni na saba da cika alƙawari, kasancewar tsohon aikin dana bari na Banki mun samu horo kan tabbatar da alƙawari, musamman idan aka tsara haɗuwa ko zuwa wani wuri, idan ka makara a Banki tara ma ake cin mutum koma kora, na saba da wannan tarbiyar. Zuwa wannan masana’antar sai na tarar babu irirn wannan tsarin, sai kuyi alƙawari da Jarumi ƙarfe takwas ko tara ba zai fito ba sai ƙarfe sha biyu. Rashin girmama lokaci shi ne babbar matsala, Ga kuma rashin tsayawa kan Magana ɗaya, idan nace kaza sai ace ai ba haka ba ne su ana su tsarin idan ka faɗi Magana zaka iya sauyawa ni kuma ba haka na ke ba. Ko shakka babu na gamu da ire-iren waɗannan matsaloli na rashin cika alƙwari da rashin jajircewa, na sha wuya kafin sabawa da wanann tsari, Akwai wani abokina ana ce masa Kast yana yawan cewa na dai na wannan ɗabi’ar tawa nace ai ni na saba da ita bazan iya sauyawa ba.

Kannywoodtoday: Tauraron fina-finan Hausa ya fara haskawa an fara kallonsa a kudancin ƙasarnan dama ƙasashen waje, ya kake kallon rashin ilimi da wasu masu wannan sana’a ke fama dashi, ko wane gudunmawa kuka fatan shirgarwa domin samun ƙarin damar inganta harkar ilimi a farfajiyar masana’antar shirya fina-finan Hausa?

Yareema: Ko shakka babu ilimi yana da muhimmacin gaske a kowace harka bama fina-finai kaɗai ba, gaskiya akwai masu raunin ilimin acikin masu gudanar da wannan harka, duk da cewar akwai masu ilimin amma dai samun ƙarin horo kan sana’ar da kake yau da kullum shi zai ƙara tabbatar da Natijar sana’ar, abinda za kayi da mai ilimi daban ne da wanda bashi da ilimi, ba wai nace ba suda ilimi ba ne, a’a akwai masu ilimi amma akwai matakin da ya kamata ace an kai. Akwai waɗanda horo kawai suke buƙata ko wani taron ƙarawa juna sani da ake buƙatar samarwa domin ƙara wayar da kan masu wannan sana’a.
Misali zuwa na Togo na ga wani abin mamaki wata mace muka samu a wani wuri a zaune idan kaga ɗan skeet ɗin dake jikinta abin akwai ban mamaki, amma ko ka san Alƙur’ani na iske tana karantawa kuma karatu ingantacce, idan anan ne abinda kawai za’ace lokacin da aka ganta cikin irin waccan shiga Arniyace kawai, saboda mu’amillar mu dasu ba ɗaya bace, su rainon Faransa ne mu kuma na rainon Ingila ne don haka ilimi ne kaɗai zai warkar da mutum daga irin wancan hange. Saboda haka dole masu kallon mu su yi mana uzuri, musamman yadda ake mana fyaɗar ƴaƴan kaɗanya, cewar kowa ɗan iska ne, ina tabbatar maka da cewa akwai ustazai da yawa acikinmu, ina jadadda maka cewar kashi 90% na ƴan fim mutanen kirki ne.
Kannywoodtoday: Shin ko Yareema na da wani gwani da yafi son fita a fim tare dashi mace ko namiji?
Yareema: Ni kowa na wane kuma ina jin daɗin fita fim da kowa, domin wani saƙo muke son isarwa, don haka duk abokan sana’ar tamu ni ina jin daɗin fita fim tare da dasu, ni yanzu nake tasowa saboda haka kowa nawa ne kasancewar sana’ace bawai sha’awa bace kawai , sana’a ta kuwa akwai wanda zance ba zanyi dashi ba? Riga ce duk wadda aka bani zan saka banda abu ɗaya…

Kannywoodtoday: Ya kake kallan batun satar fasaha da har yanzu aka kasa shawo kanta, shin ko ya kake kallon wannan matsala?

Yareema: Matsalar satar fasaha wata masana’anta ce zan iya cewa mai zaman kanta, mutane ne da sunfi ƴan fim ɗin kuɗi wani lokacin da ƙarfi, ko kama su akayi sai kaga an sake su kafin wani ɗan lokaci, saboda suna da ƙarfi, idan da shawarata za ɗauka zama za’ayi dasu da kuma gwamnati, a tattauna me yasa suke abu kaza su faɗa, sai samo maslaha adaidaita ba abu ne na faɗa ba, ko tada hankali ba, a’a muzauna gamu gasu a tattauna, tunda akwai abinda idan kayi faɗa baka samu ba sai ayi sulhu. Ina tabbatar maka da cewa suma sana’a suka ɗauki satar fasahar kuma kuɗi suke samu amma da guminmu suke yi.

Kannywoodtoday: Shin Yareema nada wata sana’ar ne ko harkar fim da waƙa kaɗai ya maida hankali?

Yareema: Alhamdulillahi kamar yadda na fara faɗa maka tunda farko cewar ni da farko ma’aikacin Banki ne, daga baya na bari don ƙashin kaina domin dogaro dakai, kasancewar ina fatan ganin na bayar da tawa gudunmawar ga ci gaban al’ummarmu musamman Hausawa, to sai na fuskanci harkar fim nada matsayi a fuskar matasa wanda idan akayi amfani dashi za’a isar da saƙonni masu yawa. Haka kuma ina gudanar da sana’ar shirya wuraren tarukan biki da makamantansu, sai kuma gabatar da wasu shirye shirye ta hanyar wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu kamar abinda ya shafi yaƙi da matsalar yoyon fisari, polio da sauransu.

Kannywoodtoday: A ƙarshe taya mai buƙatar ganin Yareema zai iya saduwa dashi musamman ga wanda ba a Kano yake ya zaune ba?

Yareema: Alhadulillahi ni a Kano na ke zaune kuma ofis ɗina yana na kan titin zuwa Gidan Zoo bayan gidan Buhari, Habiba House wanda duk yazo zai same ni Insha Allah.

Kannywoodtoday: Mun gode.

Yareema: Nima na gode.

 

Daga Shafin Kannywoodtoday

Want Ur Music/Video On HausaTop? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.