Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Cikakken Tarihin Masana’antar Kannywood Tundaga Farkon Kafata

0 34

Duniyar fina-finan Hausa, tana cike da dinbin tarihi tare da al’amurra iri-iri. Ta samo asali ne shekaru da dama da suka wuce, sakamakon wuni yunkuri da wasu matasa na wancan lokaci suka yi domin samar da fina finai a cikin harshen hausa.

Matasan wadanda kungiyar wasan
kwaikwayo ta “Tumbingiwa” ta haifar,
yawanci sun samo sha’awarsu ne ta hanyoyi biyu, wato ta hanyar gidajen Talabijin na Kano da Kaduna.

Hanya ta biyu kuma ita ce hanyar
kallon fina-finan silima, musamman na indiya. Irin wadannan matasa na wancan lokacin sun hada da Alh.
Auwalu Marshal, Adamu Kwabon
masoyi, Ado Isah Ringim, Ibrahim M. Mandawari da sauransu. Don haka ne a 1990 suka samar da fim din Hausa na farko cikin Kaset din bidiyo,
wanda aka yi wa taken “Tirmin Danya”. Tun kafin wannan lokaci akwai wasu matasa da suka yi ta yunkurin samar da fina finan Hausa , kumar su Hamisu Gurgu, sanin Lamma, Sidiya (Bakar Indiya) da sauransu,sai dai fina-finan
nasu ba su fito kasuwa ba.

Ta bangaren finan finan Hausa kuwa a cikin faya-fayen “Reel” wato irin na silima a wancan lokaci, na san an yi fina-finai irin su “Baban Larai” wanda gwamnatin jihar arewa ta wancan lokaci ta dauki nauyi, da “Shehu Umar” wanda marigayi Adamu Halilu ya shirya da “Mama learns a lesson” da kuma fim din
“Amarya”. Daga baya kuma wato Tsakanin 1980, wasu fina-finan a cikin faya fayen “Reel” suka sake fitowa, kamar su, “Ruwan Bagaja” wanda Ramalam Nuhu ya shirya, sai Maitatsine,
na Sule Umar. Da kuma “Kulba na Barna na hukumar Fina-finai ta kasa wato “Nigerian Film Corporation”.

Saura da me, tarihi ba zai manta da Gidajen talabijin na arewacin kasar nan ba, domin in akwai wata makaranta ta koyar da sana’ar fim a arewa a wancan lokacin, to wadannan gidajen ne. Furodusoshi irin su Inuwa Hassan (NTA Kano) Ibrahim Abba Gana (NTA Sokoto ) Ibrahim Boy ( NTA Kaduna) A.A. Kurawa ( CTV67-Kano) da sauransu duk sun yi matukar kokarin inganta fina-finan Hausa, wanda a wancan lokaci ake
kira wasan kwaikwayo. Na san za’a iya tunawa da “Magana Jari ce” ( NTA Kaduna) ko biri ya karye, ( NTA Kano) “karkuzu” ( NTA Jos) “Bakandamiya” ( NTA Sokoto ) da sauransu.

Karshe ina so a fahimci cewa na bayar da tarihin nan ne a takaice, domin na baya Su samu bayanin yadda aka fara. Tarihin zai zaburar da su don su bayar da ta Su gudunmuwa a na su lokacin. Wannan harka da aka fara cikin
mawuyacin hali, cikin rashin isassun kudi, cikin rashin kwakkwaran ilimin sana’ar, cikin rashin goyon bayan gwamnati da jama’ar gari, yau ga shi an
tabbatar da cewa a jihar Kano kadai akwai masu cin abinci a wannan sana’a sama da mutun dubu goma.

Want Ur Music/Video On HausaTop? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.