Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Dalilai Guda 3 Dasukasa Yan Nigeria Suke Tunanin Buhari Baiyi Musu Komai A Gwamnatinsa Ba

0 10

Tun daga ranar dimokaradiyya ta kasa, mafi yawan al’ummar Najeriya sun bayyana ra’ayoyin kan abunda gwamnatin shugaba Buhari ta shuka tsawon shekaru biyu, sai dai kashi 55 suka ce gwamnatin ta fadi, cewar su babu wani abun azo a gani da gwamnatin tayi, to sai dai wani matashi mai sharhi a harkokin siyasa ya bayyana dalilai 3 da yasa wasu daga cikin al’ummar Najeriya suke ganin gazawar gwamnatin shugaba Buhari.

 

1. A Lokacin yakin neman zabe shugaba Buhari ya bayyana kudurori da yawa ciki hada rage farashin man-fetur, sauke farashin kayayyaki abinci, samar da ayyukan yi, habaka harkar noma da kiwo da sauran kudurori; bayan Buhari ya dane kujera sai wasu daga cikin al’kawuran nashi suka gagara musamman fannin saukar da farashin kayayyaki masarufi da kuma na man-fetur.

 

2. Shugaban kasa Muhammad Buhari bai yi sa’an ‘yan majalisun dattijai ba, hada na wakilai da sauran mukarraban gwamnatinsa ganin cewa manufar su daban yake da nashi.

 

3. Tun da farko dai manyan kasar nan basa kaunar ganin Buhari a matsayin shugaban kasa, talakawa ne kadai ke da wanna burin kuma Allah ya karba addu’an su, kuma wadannan manyan zasu yi duk yadda zasu yi ganin sun durkusar da dukkan yunkurin gwamnatin Buhari na kawo duk wani ci gaba a kasar nan ta fannoni da dama kuma zasu iya kawo masa tikas wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

 

Kamar yadda HAUSATOP.com ke da labari idan kuka lura da wadannan dalilan 3 lallai zaku gane al’ummar Najeriya baza su taba gane irin alherin da shugaba Buhari ya kawo kasar nan ba.

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.