Arewa No.1 Online Portal, Hausa Hip Hop, Music, Videos, Entertainment, Lyrics, Kannywood, News

Dalilin da yasa na dakatar da abokaina daga yunkurin fitar dani a gidan yari – Inji Obasanjo

1 13

Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo a yau Juma’a, 8 ga watan Disamba ya bayyana yadda abokaninsa na kasashen waje suka kusan kubutar da shi daga gidan yari da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Ya yi wannan bayanin ne yayin da yake jawabi a bikin shekaru 20 na tunawa da marigayi Shehu Musa Yar’Adua, wanda ya kasance Manjo Janar (mai ritaya) kuma mataimakin Obasanjo a lokacin da yake shugaban kasa daga 1976-1979.

A cewar Obasanjo, ya dakatar da abokaninsa na kasashen waje daga kubutar da shi, lamarin da bai amince da shi ba domin ba zai bar kurkuku ba idan sun yi ƙoƙarin kutsa cikin gidan yari.

Majiyar HausaTop ta tabbatar da cewar, Obasanjo ya ce lokacin da aka tura shi kurkuku, “Wasu abokina daga kasashen waje sun aika da sako cewa sun shirya don kutsa a cikin gidan yari na Yola don kubutar da ni da jirgin sama mai saukar hangulu, daga nan kuma za a kai ni Kamaru, amma na ce a’a, idan kunyi hakan , ba zan bar kurkuku ba “.

Idan dai baku manta ba tsohon shugaban kasar ya kasance a kurkuku daga 1995 zuwa 1998 akan zargin cewa yana da hannu a yunkurin juyin mulkin gwamnatin soja ta marigayi Janar Sani Abacha.

1 Comment
  1. Anonymous says

    RABI.U YAHAYA GUDU

Leave A Reply

Your email address will not be published.