Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Gobara Ta Tashi A Sashen Majalisar Dattijai

0 106

An samu tashin gobara a bangaren ajiyar kayan na’urori dake majalisar Dattijai a yau din nan kamar yadda majiyarmu ta Premium Times ta rawaito.

Majiyarmu ta kara da cewa tuni Sanatoci da ma’akatan sashen da gobarar ya auku suka soma ficewa daga wajen don gudun kada hayaki ya turnike su.

Duk da cewa majiyarmu ba ta tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba, amma wani da yake sashen ya tabbatar da cewa gobarar ta samo asali ne daga bangaren na’urorin sanyaya daki na majalisar. Sannan kuma yanzu haka jami’an kashe gobara na kokarin kashe gobarar.

#Rariya

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.