Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Kannywood: Babu Namijin Daya Isa Naji Tsoron Shi – inji Maryam Gidado (Babbar Yarinya)

0 16

Maryam Babban Yarinya A Hirarta da Leadership Hausa.

Maryam Jibril, wadda aka fi sani da Maryam Gidado tana cikin fitattun jarumai mata da suke haskawa a masana’antar finafinan Hausa kuma ta dade ana damwa da ita. Amma dai daukakarta ta fara ne a lokacin da ta taka muhimmiyar rawa ita da Adam A. Zango a wani fim mai suna ‘Babban Yaro’.

Tun daga nan ne ta shiga sahun manyan jarumai da ake damawa da su a fagen shirin fim na Kannywood. Domin jin tarihin rayuwarta da kuma inda ta fito, kuma ina ta dosa, wakilinmu a Kano ya tattauna da ita. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda Shafin ‘BIDIYO’ ya nakallato muku hirar tasu:

Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu.

To ni dai sunana Maryam Jibril Gidado, wacce aka fi sani da Maryam Babban Yaro. Kuma na samu wannman suna e tn daga lokacin da muka yi fim da Adam A. Zango mai wannan sunan daga nan sunan ya bi ni ake kira na da haka.

Tarihin Rayuwa fa?

A takaice dai an haife ni Disamba 1988 a garin Jos, kuma na fara makaranta a Hassan Memorial, sai kuma aka saka ni a firamare LGA Gangare, sai na yi makarantar Arabiyya ta Sakandire a Bauchi Road, duka a Jos. Sannan na je na yi Diploma a bangaren kwamfuyuta a wata makaranta daban. To daga nan na dawo Bauchi na nemi na yi HND. Ban samu ba sai na kara yion diploma a nan ma a bangaren dididdiga. Sai kuma na ci gaba na yi HND a nan sai kuma na koma jos na yi digiri na a jami’ar Jos. To wannan shi ne ta bangaren karatu.

Maryam Gidado

Ko Maryam ta taba yin aure kuwa?

Tooohhh! (Dariya) yanzu idan na ce ma ban taba yin aure ba sai a yi min dariya a matsayina na Bafulatana, don kowa dai ya san ka’idar Fulanin daji ne lokacin bayan na gama WAEC da NECO na lokacin ina shekara sha uku aka yi min aure. Ina shekara sha hudu ha haifi yarinya bayan shekara daya da auren kenan. Don haka shekara goma sha hudu na ba ‘yata ta faro kenan a duniya. Yanzu ka ga ta shiga shekara sha daya kenan ‘yata ta farko.

To ya ya aka yi kika samu kanki a farkar fim?

Ni dai gaskiya da ina kallon fim ne tunanin shirme ne, domin idan na ga ‘an fim har zaginsu nake yi don ban taba tunanin zan yi fim ba. Don ‘yar’uwata ita ta so yin fim Allah bai yi ba, don kanwata ce ta zo ta dan fara ba a san ta ba sai ta tafi. To da yake lamarin na Allah ne ita ba a santa ba a harkar fim sai ni aka snai. To daga baya sai na ga yadda bain yake da yadda ake fadakarwa. Na ga wasi ma sin musulunta ta hanyar fim. Sai na ga abin wa’azi ne.

To a baya kin fada mana yadda aka yi miki aure har kika haihu. Sai dai ba ki fada mana ba ko kun rabu da mijin ko mutuwa ya yi ko kuma kina da aure yanzu kike in fim?

To haka ne (dariya) kai gaskiya ba zan iya fada ba. Saboda a duniya babu abinda ya kai sirri dadi. Idan ka rufa wa wani asiri Allah zai rufa naka. Kuma tsakanin mata da miji sai Alla. Don haka wanan mutane su yi hakuri. Su kansu sun san gaskiya na fada ba karya na yi ba. Don haka rufa asiri yana da kyau.

Shin wannan dan naki na biyu babansu daya da ‘yar ki ta farko?

Ba ubansu daya ba. Bayan mun rabu da si ne na auri babansa. Shi lokacin da na auri babansa ma har na fara harkar fim muka yi aure. Ina da cikinsa ya gudu ya bar ni har na haife shi yanzu shekarun dana na biyu bakwai kenan.

Abin nufi a nan shi ne, kun rabu da shi ne ko rasuwa ya yi?

To in dai wannan ne ba rasuwa ya yi ba, yana nan da rans.a sannan kuma sai da ina da cikin dana na biyu wata daya ya tafi ya bar ni yanzu shi ma yaron na haife shi shekarasa bakwai har yau bai zo wajen da yake ba. Sai dai ya turo a dauke shi da hotonsa kuma zai iya kira ta waya su yi magana, amma dai yana nan a Kaduna kawai dai tafiyar da ya yi ya bar ni don wani dalili ne na daban. Don haka ‘ya’yana biyu, don na fada maka auren fulani da wuri ake yi shi ya sa na haifi ‘ya’ya biyu.

To daga nan sai me ya biyo baya?

Kai dai a bar maganar haka, don sirri yana da dadi.

Sai ki fada mana yadda aka yi kika samu kanki a harkar fim da kuma shekarar da kika fara?

A gaskiya na manta shekarar da na shigo, amma dai na fara ne da album din Mahmud Nagudu mai wakar ‘Garin So Nisa,’ amma fim din da aka fara yi min shi ne wani fim ‘Ragowar Yaki,’ lokacin da muke yi a Jos da ni eda Ali Nuhu. Shi ne fim dina na farko da na fara yi a duniya, kuma daman tunda na fara fim ban fara da mai tallafawa jaruma ba da jaruma na fara ba. Kodayake da farko mutane sun dauka album nake yi ba fim ba, saboda shi ne na fara. Sai daga baya na zo na shiga na su Alma na yi ‘Ragaya,’ na yi ‘BIngyal,’ ‘Mukaddari’ da sauransu.

Ko za ki iya fadar yawan finafinan da kika yi?

Gaskiya ba zan iya fadar adadinsu ba. Don ka ga a wata zan iya yin fim biyu ko uku, to ya ya zan iya snain fim din da na yi a tsawon lokacin da na yi a harkar fim? Sai dai zan iya fadar wasu kadan daga cikinsu, musamman na ‘yan kusa haka kamar ‘Babban Yaro,’ ‘Wata Hudu,’ ‘Munafikin Mata,’ ‘Al’ajabi,’ ‘Mukaddari,’ ‘Zawarawa,’ ‘Fulani,’ ‘Sultan,’ ‘Basaha,’ wadannan su ne zan iya fada kuma ina ji da su a cikin finafinaina.

Akwai lokacin da kika yi wani tashe sai kuma aka daina ganin ki a harkar fim. Hakan ya sa ake cewa ko kin yi aure ne, ko kuma harkar kika bari.

To gaskiya ba aure na yi ba, kuma ba barin harkar na yi ba, ina yi kadan ne sai dai mutane ba za su gane ba, saboda ba sa gani na sosai, amma dai kafin na fara sai da na fada wa mahaifina sai ya ce shi ma ga dokar da zai kafa min ya ce makaranta yake so na yi, kuma na matsa zai na yi to da na ga na smau wannan sunan na daukaka sai na koma makaranta. Hakan ta sa ake ga nin kamar na bari ne, amma dai ina yin fim lokaci zuwa lokaci. Amma dai yanzu na gama na dawo.

sannan a baya an fi ganin ki tare da Adam A Zango, amma yanzu ba a ganin ku tare kamar a lokacin baya.

To ai daman ba a kamfanin Adamu nake ba, kuma kamfanin Adamu finafinan da suka yi min ba su da yawa. Sai dai su ne suka yi min fim din da ya fara daga ni. Don bayan album din Mahmud Nagudu babu wani fim da ya daga ni sai na su Adamu. Kuma sannan furodusa ne yake hadawa ba wasu ba ne suke hada ku. Don haka idan suka ga dama su hada ni da Ali, in suka ga dama su hada ni da Adamu, ko Sani D Danja da sauransu.

Yanzu a matsayinki na babbar jaruma, burinki ya cika a harkar fim?

Gaskiya burina ya cika sai godiya ga Allayh. Yanzu burina daya ne kawai Allah ya ba ni miji nagari.

Ku ‘yan fim kullum kune fadar miji nagari kuke nema, amma ana yi muku kallon kuna da ruwan ido.MARYAM2

To, (dariya) ai mu ba ruwan ido muke yi ba, mu duk wanda zai zo neman mu ba ruwan ido muke ba, kawia dai muna tunanin kawai dai ya gan mu a fim ne yana son ya aure m,u don waa manufa da yake da ita. Shi ya sa muke tsoron auren, ba wai muina tunanin wane mai kudi ba ne, ko marar kudi ba. Don idan ka auri mai kudi ma zai zaci don kudinsa ka aure shi. Gara ka auri talaka idan kudin ya zo kuna tare da shi. To yanzu abin ne sai ya zama mu muna tsoron mazan, su ma suna tsoron mu.

Ba kya ganin ana cewa da ku in kun yi auren ma ba kwa zama?

To ai wannan maganar da na yi ita ce ta ba da amsar wannan tambayar na muna zama ko ba ma zama. Nan za a gane Allah ne ya san dalilin rabuwar tsakanin mata da miji, ba mamaki wancan dalilin zai sa a zo a yi auren wani bai yi tunanin wannan ba sai haka ta kasance.

Bayan harkar fim, ko akwai wata harka ta kasuwanci da kike yi?

E, ina yin kasuwanci. Don yanzu ina da wajen gyaran gashi a gidanmu. Sannan a makarantarmu ina yin aiki na wucin gadi kuma ina zuwa ina saro kaya haka na mata ina sayarwa.

Akwai wani lokaci da kika shirya na barin harkar fim?

Gaskiya ban shirya ba, sai lokacin da Allah ya kawo min miji to lokacin zan bar harkar fim.

Me kike alfahari da shi a game da harkar fim?

To abinda nake alfahari da shi na san ko ban yi komai ba akwai wa danda suka karu da ni a kan wani fim da na yi na gyara tarbiyya, sannan kuma na san mutane wanda yake duk abin alfahari ne wanda ba kowa Allah yake wa haka ba. Sannan na samuw asu abubuwa wanda yake hakkina ne nake ci ba na wani ba. To sannan kuma da fim na je Makka na yi gida da wasu abubuwa, kuma da his nake karatu, don haka dole na yi alfahari da harkar fim.

To mene ne sakonki na karshe ga masu karatu?

Sakona na karshe shi ne, masoyanmu da kuma maganar da ake fada ba ni ma zaman aure don Allah su daina fada. Ba haka ba ne, duk rashin fahimta ne da rashin zuwan su kusa da mu. Don haka idan sun ga mun yi kuskure su rinka sanar da mu ko ta hanyar mujallar fim ne, kuma su rinka tambayar abin da ya shige musu duhu a game da mu, su daina yi mana shaci gadi, su rinka sanar da mu kurakuranmu.

Want Ur Music/Video On HausaTop? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.