Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Kannywood: Fim Din Rariya Yasamu Karbuwa Wajan Matasa

0 15

Kamar yadda aka kwashe kwanaki ana tallata fitar shararren fim ɗin nan mai suna RARIYA, yau Litinin aka fara haske shi agidan Cinema na katafaren wurin sayar da kayan taɓa ka lashe mai suna Shopwhirte dake Ado Bayero Mall kan titin zuwa gidan Adana namun daji na Zoo. Babban abinda ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda jama’a maza da mata yara da manya ke tururuwa a ƙofar wannan wuri. Sannan kuma ga jami’an tsaro kamar ƙasa. An tsara yadda jami’an tsaron ke tantance duk mai niyyar shiga wurin kallon.

Dan dazon jama’a gun shiga Cinema dan kallon fim ɗin Rariya.

Kamar yadda aka tsara akwai lokuta daban daban da za’a ci gaba da nuna fim ɗin kuma farashi daidai aljihun ka, kama daga Naira ₦500 har zuwa Naira ₦1500 a ranakun mako. Fim ɗinan sha alwashin zai ƙayatar da masu kallo sannan kamar yadda wurin ya fara ɗaukar harami ana sa ran tara maƙundan kuɗaɗe alokacin nuna fim ɗin Rariya. Babban abinda yanzu ake jira shi ne jama’a idan sun kalli wannan fim wane sharhi zasu yi masa. Duk da cewar an yiwa manema labarai fuskar shanu. Domin babu wani rangwame da aka shiryawa ‘yan jarida duk da sune suke tallata ƙasaitar fim ɗin na Rariya.

Wasu daga cikin matasa da sukaje kallon Rariya.

Jarumi Nuhu Abdullahi nayiwa ƴan jarida jawabi agun Cinema kafin shiga kallon fim ɗin Rariya.

Za dai a nuna fim ɗin Rariya a Legas, Fatakwal, Ibadan, Kalaba, Akure da Kano.

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.