Arewa No.1 Online Portal, Hausa Hip Hop, Music, Videos, Entertainment, Lyrics, Kannywood, News

KANNYWOOD: Jarumi Ali Nuhu Ya Aiwatar Da Wani Babban Abun Bazata A Cikin Azumi.

0 2

Ali Nuhu yanata shan yabo a idanun duniya. domin wannan shine karo na biyu da Ali Nuhu ya rabawa mabukata kayan abinchi tun kamawar wannan azumin.

Jarumin ya raba gero da shinkafa acikin birnin kano a yankin Dala. Ali Nuhu ya raba wannan kayan masarufine domin kyautatawa masu karamin karfi, wanda Allah bai horewa sukuni ko wadata ba.

Wannan abin alkhairi da Ali Nuhu ya yi ya janyo ma shi samin yabo agurin shugaban hisba na kano Malam Aminu Daura,Kuma Malamin yace ya kamata sauran jarumai suyi koyi da Ali Nuhu kodan samin lada mai yawa.

Dandalin HausaTop.com ta samu labarin cewa Ba wai Ali Nuhu bane kawai ya yi irin wannan sadaka ga marasa wadata. Sani Danja, Mansura Isah, Adam A Zango duk sunyi rabon kayan abinchi ga masu karamin karfi a wannan watan.

Malam Ayuba Dala yana daga cikin wanda ya sami buhun gero dana shinkafa wanda jarumi Ali Nuhu ya raba. kuma ya nuna farin cikinsa afili, sannan ya yi godiya amadadin sauran. Muna fatan Allah ya sakawa Ali Nuhu da alkhairi ameen.

Leave A Reply

Your email address will not be published.