Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Kannywood: Sabbin Jarumai Guda 5 Wanda Tauraruwar Su Tafara Haskawa a Wannan Shekarar 2017

0 26

Sunayen sabbin jarumai 5 dake tashe a dandalin kannywood a halin yanzu ciki har da shaharraren mawakin hausa. Tauraron su na haskawa kuma da alama sun shirya damawa da sauran fitattun jarumai dake masana’antar.

Kwanan baya Wani malami harkan shirya fina-finai Farfesa Abdullahi Uba Adamu yace daya daga cikin kalubalen da kannywood ke fuskanta shine yawan fitowa wasu tsirarrun jarumai fiye da kima a fina-finai. Ga jarumai kamar haka:

1. Rashida Lobbo : Tana cikin jarumai da suka amshi kyauta a bikin karrama jarumai da mujallar city people ta shirya a jihar Legas cikin wannan shekara

2. Maryam Yahya : Tun fitowar ta a cikin shirin “Mansoor” wannan jarumar ta samu karbuwa a farfajiyar kannywood domin bayan fitowar a shirin ta samu damar fitowa a fina-finai da dama. Dalilin da ya sanya ta zama jarumar shirin Mansoor. Matashiyar wanda ta shigo farfajiyar yin fim da kafar dama ta shaida wa BBChausa cewa Ba harkar fim kadai ke gabanta. Latsa nan domin karanta dalilin “Ba harkar fim kadai ke gabana” – inji jaruma.

3. Umar M.shareef : Shima wannan mawakin ya garzayo farfajiyan yin fim kuma tun bayan fitowar sa a “Mansoor” masu shirya fina-finai na Kannywood sun kara bashi damar fitowa fina-finai daban daban. Zai kara haskawa a cikin watni sabon fim mai suna “Mariya” tare da abokiyar aikin sa na cikin shirin “mansoor” watau Maryam yahaya.

4. Amal Umar : Wannan matashiya ta haska a fina-finai daban daban kana tana damawa da jiga-jigan gwarzayen masana’antar

5. Garzali Miko : Babu shakka wannan matashin jarumi ya shirya bayyanar da basirar shi na yin fim kuma da alamu direktoci sun gani a jikin shi

Want Ur Music/Video On HausaTop? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.