Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Kannywood: Sani Danja Yabiyawa Jaruma Fati Washa Kujerar Umara

0 28

Hajiya Fati Washa tana daga jerin Hajiyoyin da zasu koma Saudiyya abana, idan taje wannan karon zuwanta sau uku kenan. Abinda yaba mutane mamaki shine jarumi Sani Danja shine ya biya masu kujera ita da matarsa Mansurah Isah da kuma matar Yakubu Muhd.

Cikin masana’antar hausa fim da wajenta anata yin cece-kuce da muhawara akan dalilin da yasa Danja ya biyawa Fati Washe kujerar Saudia, wasu suns cewa soyayyace atsakaninsu wasu kuma suna cewa sabida Mansurah Isah ya biyawa Fati Washa kujera.

Ganin anata cece-kuce shine dalilin da yasa muka kira Sani Danja awaya dan jin gaskiyar lamari. Danja ya sanar damu cewa: gaskiya babu wata soyayya tsakaninsa da Fati Washa, idan ma akwai to sai sai ta musilimci. Acewar Danja ya biyawa Fati Washa kujerar Saudia ne sabida matarsa Mansurah Isah. Domin tun bayan auren mu da Mansurah bata da wata Aminiya a kannywood kamar Samira Ahmed da kuma Fati Washa. Dan haka na biyawa Fati  Washa kujerar Saudiyya.

Wannan maganar da Sani Danja ya yi ta gamsar da wasu, amma wasu har yanzu basu yarda ba. sunce tabbas akwai dalilin da yasa Danja ya biyawa Fati Washa kujerar Saudiyya amma ba wanda ya fada ba. Domin amajiyya mai kyau ta jaridar Premium Time ta tabbatar da cewa Mansurah bada son ranta Danja ya biyawa Fati Washa kujerar Saudiyya ba.

Mu dai aikin mu bibiya idan tayi wari zamu sanar da ku.

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.