Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Kar Ku Siyar Wa Buhari Makamai, Kashe Mu Yake – Yan shi’a Sun Roki Amurka

0 5

Image result for Kar Ku Siyar Wa Buhari Makamai, Kashe Mu Yake - Yan shi'a Sun Roki AmurkaKungiyar nan da ke kiran kansu ta yan uwa musulmai mabiya tafarkin shi’a a Najeriya watau Islamic Movement in Nigeria (IMN) a turance sun rubutawa gwamnatin kasar Amurka takardar korafi suna mai shawartar ta da kar ta sayar wa shugaba Buhari makamai da wasu kayan soji.

Takardar da yan shi’ar suka rubuta a ranar 17 ga wannan watan na Agusta, shekarar 2017 kuma shugaban kwamitin nan dake neman a saki Zakzaky ya sanyawa hannu sun rubuta cewa sojojin Najeriya suna kashe jama’a ne kawai.

Kar ku sayar wa Buhari makamai, kashe mu yake - Yan shi'a sun roki AmurkaHausaTop.com ta samu kuma cewa a cikin takardar da yan shi’ar suka rabawa manema labarai irin ta, sun kuma rubuta cewa sojojin Najeriya a karkashin mulkin Buhari din ba su darata yan cin dan adam ko kadan.

Haka kuma yan shi’ar sun ja hankalin hukumomin kasar ta Amurka da cewa duba da yadda sojojin suka kashe yayan ta 34 a shekara ta 2014 kafin daga bisani su kashe wasu daruruwan a karshen shekara ta 2015, mai dace ace an kara saida masu da makaman ba.

 

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.