Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

KARANTA KAJI: LAafiyar Shugaba Buhari Dakuma Ranar Dazai Dawo Nijeria

0 3

Majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai dawo a karshen wannan mako ba a baya an ce shugaban kasa Buhari zai dawo daga birnin Landan inda yake jinya.

 

Shugaban kasa ya bar gwamnatinsa a hannun mataimakain sa Yemi Osinbajo sannan ya tafi jinya a birnin Landan Majiyar gwamnatin tarayyan Najeriya ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai dawo Najeriya daga birnin Landan a karshen wannan makon ba kamar yadda fadar shugaban kasar ta rahoto a baya. Shugaban kasa Buhari ya bar kasar zuwa birnin Landan wata daya da ya wuce inda anan yake jinya da ganin likita.

 

Daily Mail ta ruwaito cewa likitan shugaban kasar ya kaddamar da cewa ya zama lallai Buhari ya yi wani gwaji a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni.

A cewar majiyoyin, likita ya ce gwajin ne zai yanke shawarar ranar da zai komo kasar.
A baya Dandalin Mujallarmu.com ta rahoto cewa Sahara Reporters tayi ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo gida Najeriya a mako mai zuwa.
Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.