Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Karanta Kuji Yadda Wani Ya Kashe ‘Yar Yayansa Kan Bashin Naira Dari

0 6

Image may contain: 2 people, hat and closeup

Al’umar Unguwar Rimi da ke garin Keffi a karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa, sun shiga alhini biyo bayan rasuwar wata budurwa mai suna Amina Abdullahi da aka fi sani da Ummi sakamakon bugu da ta sha a hannun wani matashi kuma dan’uwanta mai suna Hamisu wanda kani yake ga mahaifinta.

A safiyar Larabar da ta gabata ce aka ce marigayiyar ta je bin bashin kudinta naira 100 a hannun Hamisu, wanda a karshe lamarin ya sauya ya koma fada da har ya kai ga Hamisu ya lakada wa Amina dukan tsiya, lamarin da daga bisani ya yi sanadiyyar rasuwarta.

A cewar wata majiya mai tushe, ko da Amina ta yanke jiki ta fadi sakamakon bugun da ta sha, da farko an dauka suma ta yi, amma duka matakan da aka dauka don ganin ta farfado hakan bai amfana ba. Daga bisani, haka aka kwashi Amina zuwa wani asibiti da ke kusa inda a nan aka tabbatar da rasuwarta.

Ya zuwa hada wannan labari, Hamisu na can kwance gadon asibiti sakamakon somewa da ya yi bayan da ya samu labarin cewa Amina ta cimma ajalinta sakamakon dukan da ta sha a hannunsa.

Binciken wakilinmu ya gano cewa, marigayiyar na shirin amarcewa bayan babbar sallah da makonni biyu tare da saurayinta Nasiru Ibrahim, sai kuma ga shi Allah ya yi ikonSa.

*a dayan hoton marigayiyar ce da saurayin da za aura, Nasiru Ibrahim

Want Ur Music/Video On HausaTop? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.