Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Ko Buhari Ya Sake Malamin Mu Ko Kuma Ya Sake Komawa Landan Jinya Ba Shiri – Inji yan Shi’a

0 6

Ko Buhari ya sake malamin mu ko kuma ya sake komawa Landan jinya ba shiri - Inji yan Shi'aWasu yan Najeriya almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky wadan da aka fi sani da yan shi’a sun gudanar da wani taron gangami da zanga-zangar lumana a garin Yola dake a jihar Adamawa inda suka bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya sake masu jagoran su ko kuma ya sake komawa yar gidan jiya.

Su dai yan shi’ar wadan da suka yi jerin gwano mazan su da matan su tsofaffin su da yaran su sun yi wannan zanga-zangar ce bisa titunan birnin na Yola yayin da kuma suka ziyarci ofishin nan na hukumar kare hakkin dan adam dake a jihar.

HausaTop.com ta samu cewa a wajen zanga-zangar, an ga da yawan su suka yin maganganu na kin jinin gwamnatin tarayya da kuma shugaba Muhammad Buhari wanda a halin yanzu yake ci gaba da rike shugaban nasu sama da shekara daya da rabi.

Mun dai samu cewa wasu daga cikin yan shi’ar sun yi yin kamalai marasa dadi ga shugaban inda wasun su ke cewa ko dai Buhari ya saki malamin nasu ko kuma ya koma birnin Landan babu shiri.

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.