Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

NEWS: Gwamnati Ta Fara Biyan Kudi Masu Tsoka Ga Duk Wanda Ya Gano Barayin Gwamnati

0 6

A karon farko gwamnatin Najeriya ta biya masu tona asirin barayin gwamnati, inda ta biya mutum 20 naira miliyan 375,875,000.

Kawo yanzu, gwamnatin ta kwato Naira biliyan 11,635,000,000 a sakamakon wannan tsari da aka fito da shi a watan Disamban bara.

Ministar Kudi ta Najeriya Kemi Adeosun ta ce: “Wannan shi ne karon farko da muka biya wadannan kudaden a karkashin shirin nan na masu tona asirin barayin gwamnati, kuma yana nuna jajircewar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari game da cika alkawurra… “.

Ta kara da cewa “tsarin muhimmin bangare ne na yaki da cin hanci”.

Tun farkon shekarar nan, jami’an tsaroa a Najeriya sun bankado makudan kudaden da ake zargin an boye a wurare daban-daban.

Want Ur Music/Video On HausaTop? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.