Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

NEWS: Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Mai Karfi Akan Gwamnatin Buhari A Sakon Sallah

0 12

Sarkin Musulmi mai martaba Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce ainihin makiyaya suna kiwo daga shanu zai sandunansu kawai, ba sa yawo da bindigogi.

Sarkin Musulmi a cikin sakonsa na karamar sallah wato Eid-el Fitr ga ‘yan Najeriya ya kira gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasar, Muhammadu Buhari da babban murya da su bincike inda makiyaya nan masu yawo da bindigogi ke samu makamai wanda suke amfani da ita wajen kai hare hare ga al’ummomin kasar nan.

Kamar yadda HAUSATOP.com ke da labari, Sultan ya ci gaba da cewa: “Babu shaka akwai bata gari a tsakanin Fulani makiyayan, amma wadanda ke dauke da makamai da kuma kashe-kashen ba makiyaya ne”.

“Wadanda ke dauke da makamai miyagu ne a tsakanin makiyayan, kuma ya kamata gwamnati ta dauki mataki a kan su”.

Ya kamata gwamnati ta kafa kwamitin bincike don gano inda wadannan makiyaya ke samun makamai kuma ta dauki mataki mai tsanani don rage wadannan hare-haren.

Sarkin Musulmi ya yaba wa gwamnatin tyarayya a matakan magance hare haren ta’addanci a arewa maso gabashin kasar.

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.