Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

NEWS: Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Yayi Magana Kan Mulkin Buhari

0 8

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Dr. Goodluck Ebele Jonathan yayi ammana da cewa matsalolin Najeriya ba abu ne wanda mutum daya kan iya warwaresu ba.

Tsohon Shugaban ya cigaba cewa musayan maganganu da zargi da mutanen bangarorin. Najeriya ke jefa wa juna ba zai kai kasar ga tudun na tsira ba. Sai dai, kamata yayi duk a hada karfi da karfe waje daya domin gina kasar.

Tsohon Shuga Jonathan din ya bada wannan shawarar ne ta bakin tsohon sakatare na gwamnatin tarayya Sanata Ayim Pius Ayim a wajen lecture na 5 don tunawa da marigayi Farfesa Celestine O. E Onwuliri.
Tsohon shugaba Jonathan yayi magana kan mulkin Buhari

Farfesa Celestine Onwuliri yana daga cikin jama’an da suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon hadarin jirgin sama kirar Mc Donnell Douglas 83-MD da ya faru a ranar 3 ga watan yuli na shekarar 2012 a garin Legas.

“Mutane sunyi maganganu da yawa akan matsalolin Najeriya amma ni abin da zan iya cewa shine matsalolin sunfi karfin mutum daya” Inji Jonathan.

A cikin bayanin da yayi, tsohon gwanan Jihar Imo Chief Ikedi Ohakim yayi juyayin rashin Farfesa Celestine Onwuliri da ma wasu ‘yan Najeriya. Kuma ya kara da cewa matukin jirgin ma bai da shedar tatancewa na tukin.

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.