Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Rana ba ta karya: Kano ta shirya karbar bakuncin Shugaban Kasa Buhari

0 25

Ku na sane cewa yau ne ake sa rai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya leka Jihar Kano karo na farko bayan ya hau mulki. An dai ta sa ran Shugaban zai kai ziyara a baya amma bai yiwu ba. Jiya Gwamna Ganduje ya kai har cikin dare yana aiki domin tarbar Shugaban Kasar.

A yau da gobe ne dai Shugaban Kasa zai kaddamar da wasu ayyuka da dama na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a fadin Jihar. Daga cikin ayyukan da za a kaddamar akwai asibitoci 2 da aka kammala aikin su a Zoo Road da kuma Unguwar Giginyu.


Bayan nan kuma akwai hanyar kasa da ke Unguwar Fanshekara da titin babban banki watau CBN a cikin Gari. Har wa yau akwai hanyoyin da ake ginawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai duba a ziyarar da zai kawo ta kwana biyu daga yau zuwa gobe Alhamis.

Akwai kuma wasu gidaje da Gwamantin Dr. Ganduje ki shirin fara ginawa wanda duk Shugaban Kasar zai sa hannu kamar yadda wani babban Jami’in Gwamnatin Jihar Salihu Tanko Yakassai ya bayyana a jiya. Mutanen Kano ne su ka fi ba Shugaban kuri’a mafi tsoka a 2015.

Want Ur Music/Video On HausaTop? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.