Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Sakon Goron Sallah Daga Shugaban Kasa Buharai Zuwa Ga Yan Nijeriya

0 17

Image may contain: 1 person, sitting and indoorIna mai matukar taya ku murna dukkanin ku, musamman ma Musulmai daga cikinku na wannan ranar Sallar Idi babba (Eid-El-Kabir) na wannan shekarar.

Haka kuma ina taya ‘Yan uwa musulmanmu maza da mata da suke kasa mai tsarki (Makka) a yanzu haka domin gudanar da aikin Hajjin wannan shekarar.

Amma daga farko ina so zan yi amfani da wannan damar domin in yi muku godiya bisa irin addu’oin da ku ka yi ta gudanarwa a kaina domin samun lafiyata da kuma fatar alheri da kuma murna dawowa ta Nijeriya.

Hakika addu’oinku da kuka dukufa kukaita gudanarwa akaina wacce da hanada musulmanku da kiristoci daga cikinku dama masu mabanbantan ra’ayin siyasa dama kabilu daban-daban daga cikinku, hakika sun kara mun kwarin guiwa da kara dagewata sosai dama gwaunatinmu domin gina wannan kasa tamu ta cigaba.

Daga bangaren shagalin bikin sallar layyar wannan shekarar, ina rokon dukkanin ‘Yan Najeriya da mu aje banbance-banbancen dake tsakaninmu, mu watsar da tsana da tsangwama mu rungumi zumunci da abota da ‘Yan uwantaka da kuma hadin kai domin mu ciyarda kasarmu Najeriya gaba

Daga bangaren musulmi na duniya kuma, manufar wannan bikin shine tuna irin jarabawar da ubangiji yayiwa annabi Ibrahim na yanka dansa ne da kuma irin mika wuyar da yayi wurin biyayya ga umarnin mahaliccinsa ne.

Kamar yadda muke cike da farin cikin wannan bikin, inada yakinin wannan kasa tamu zata samu cigaba cikin sauri ta kowani bangare idan mukayi koyi da halayen annabi Ibrahim ta hanyar sadaukar da kai, hakuri, son juna, kwazo da kuma biyayya ga umarnin ubangijinmu da kuma kiyaye dokokin hukuma

Dole ne mu koyawa kanmu son juna da kuma daukar kanmu a matsayin ‘Yan uwa maza da mata wadanda mukeda tarihi iri daya kuma dole ne mu zama kamar yadda wata karin magana ta ‘Yan Afrika take cewa “Iyalai kamar bishiya ce, za ta iya lankwashewa amma ba za ta karye ba”

Haka kuma har wayau dai, ina mai tabbatar muku cewar wannan gwaunatin wacce ta dauki harkar tsaron kasa, tattalin arziki da walwalar yan kasa a matsayin ababe masu muhimmanci data sanya a gaba, ba zata taba gajiyawa ba har saita cimma gurinta na samarda sabuwar Najeriya mai cike da zaman lafiya tattalin arziki mai yalwa da kuma cigaban jama’a.

Ina yi wa kowa da kowa barka da sallah kuma a yi biki lafiya.

Want Ur Music/Video On HausaTop? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.