Arewa No.1 Online Portal, Hausa Hip Hop, Music, Videos, Entertainment, Lyrics, Kannywood, News

Sarki Ya Shirya Tsaf Domin Dawowa Dan Haka Masu Gudu Su Gudu (Karanta)

0 3
Jim kadan bayan Aku uwar surutu ta bada shelar dawowar Sarkin Daji, manya da kananan dabobbi sun nutsu. Na zaune ya tashi tsaye, kowa hankalin shi ya tashi. 

Su shaho da hankaka an kasa zama waje daya. Tattabara uwar alkawari kuwa sai kai-kawo ake don ganin an daidaita sahu a daji. Su Alhuda Huda kuwa tunda zaki ya tafi rangadi ake tara bayanan sirri da za a baiwa Zaki idan ya dawo.
Su Dila hankali ya tashi domin da yiyuwa ayi waje road.

Alamu sun nuna wannan karan tsaigumin Zakanya yayi tasiri a zuciyar Zaki domin Zakanya ta tabbatar da cewa Zaki zai rufe ido yayi garan bawul.

Su Angulu dama anci hanjin jumuna, an kasa zama waje daya har bayanan sirri ya nuna cewa Angulu, Giwa, Damisa, Kura da makarraban su sun yi kokarin dana tarko wa Zaki sai Alhuda Huda ya gabatar da aikin sa na leken asiri akan wanda ya tona musu asiri a idon duniya.

Babban fatan kananan dabbobi shine suyi tozali da Sarki cikin koshin lafiya. Tare da fatan Zaki zai dauki shawarwarin da zasu sauya daji zuwa lambun fure wanda kowa zai sheka kuma yayi yawo ba tare da barazana daga dabbobi masu fika ba.

ALLAH KA DAWO MANA DA ZAKI LAFIYA.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.