Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Siyasar Kano: Jam’iyyar APC ta kwance ma gwamna Ganduje zani a kasuwa (Karanta)

0 38

Image result for kwankwaso da gandujeJam’iyyar APC ta kasa ta dauki wani mataki da ake ganin raba gardama ne akan cecekucen da ake fama da shi akan shugabancin jam’iyyar a jihar tsakanin tsagin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamna Abdullahi Ganduje.

Uwar jam’iyyar APC ta kasa ta gayyaci Umar Haruna Doguwa ne a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar zuwa taron da mukaddashin shugaban kasa yayi da shuwagabannin jam’iyyar su 36 na kasa.

Jam’iyyar ta gayyaci Doguwa ne wanda ake ganin yana samun goyon bayan Sanata Kwankwaso, duk da ikirarin da shugaban APC tsagin Gwamna Ganduje, wato Abdullahi Abbas ke yin a cewa shi ne shugaban jam’iyyar na halaliya.

BBC Hausa ta ruwaito an tattauna batutuwan da suka shafi jam’iyyar tare da rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin taron da uwar jam’iyyar ta kira da Farfesa Yemi Osinbajo.

Cikin wata hira da yayi da majiyar HAUSATOP, Umar Haruna Doguwa yace “Na halarci taron ne kamar yadda uwar jam’iyya ta saba gayyata tarukan jam’iyya a matsayin halastaccen shugaban APC na jihar Kano.”

Tun bayan darewarsa karagar mulki ne dai ruwa yayi tsami tsakanin gwamnan jihar Kaduna Abdullahi Ganduje da Sanata Rabiu Kwankwaso, hakan kuwa yayi tasiri wajen rarraba kan jam’iyyar APC a jihar.

 

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.