Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Tambayar Da Momo Ya Yiwa Umma Shehu Ba’a Muhalli Yayita Ba – Inji Gogaggun Masana Aikin Jarida

0 16

Image result for momo da umma shehuManazarta al’amuran yau da gobe musammam wanda suka kware a aikin jarida sun fadi ra’ayoyin su akan kasa amsa tambayar Aminu Sheriff Momo da jarumar fim Umma Shehu tayi.

Ra’ayin da yafi shahara shine cewa ita tambayan akan kanta ba ta muhallin ta saboda Kundin Kannywood ba wuri ba ne na gano zurfin ilmin addinin mutum, wuri ne da ake tambayoyi da suke da alaka rayuwar jarumi da sa’anar fim.

Ko wani abu yana da muhallin shi kuma ga duk mai adalci yasan filin Kundin Kannywood ba fage bane na Addini. Sannar rashin amsa wannan tambaya ba dole bane ya zama bata sani ba, zai iya yiwuwa ba ta so ya ci gaba da tambayoyi da suka shafi wannan ne.

Ya kamata mutane su sani kuma su tina da cewa Umma Shehu jarumar fim ce, ba malamar addini ba. Ya kamata mutane su dinga hukunta ta akan asasin film ba addini ba. Bajintar da mutane ya kamata su kalla shine na film, addini personal rayuwar ta ce.

Sannar mutane su sani Kannywood masana’antar film ce, ba sharadi bane mutum ya zama yana da kwarewa a addini ba, ana daukan jarumai ne saboda bajintar su a film, ba wanda yake gwada addinin wani. Kai ba sharadi bane mutum ya zama musulmi ba ma in the first place.

Kuma domin Umma Shehu ta kasa amsa tambaya ba hujja ba ce akan jahilcin Kannywood; fasali ma su jarumai rubutattun zantuka ake basu ba da kan su suke fadin abubuwan da suke fadi ba.

Sannan addini ya hore mu ba mu dinga yiwa junanmu uzuri kuma mu dinga daga kafa. Zai iya yiwuwa ta manta, zai iya yiwuwa bata gane tambayar Ba, zai iya yiwuwa bata son amsawa da ma sauran dalilai.

Want Ur Music/Video On HausaTop? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.