Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Wa’adin kamo Shekau na kwana 40: Shin Mambilar sojojin zasu ko kuwa Sambisa?

0 10

Wa'adin kamo Shekau na kwana 40: Shin Mambilar sojojin zasu ko kuwa Sambisa?A makon nan ne dai Laftanal Janar Buratai, shugaban hafsoshin sojojin Najeriya, ya kara wa jami’an Operation Lafiya Dole masu kokarin kakkabe burbushin jahilan Boko Haram bayan wa’adin kamo Abubakar Shekau, bayan da suka kasa kamo shi a watan jiya.

A yanzu dai, Janar Kuka Sheka, kakakin sojin, yace wa’adin da aka baiwa Ibrahim Attahiru, Janar mai shugabantar Lafiya Dolen, yayi nasara, domin kusan dukkanin waziran Shekau din sun shigo hannu ko kuma sun hallaka a hannun sojin Najeriyar.

An kuma halaka kananan mayaka kusan tamanin a dai wannan kwanaki arba’in. Sai dai har yanzu ba’a sami ganin Abubakar Shekau din ba, sai dai a faifan bidiyo kamar yadda ya saba. Ana kuma sa rai za’a ga sabon bidiyonsu na sallar idi a dazukan Sambisa kamar yadda suka saba aikowa, kwanaki kadan bayan kowacce sallah, saboda yada farfagandarsu.

Tambaya a nan shine, wai ina Shekau Muhammadu yake ne? A ina yake boye? Kuma me ya hana sojoji sanin inda zasu kamo shi?

Amsa dai shine, a wata makalar, an ce yana Sambisa a boye, kuma kammammen kwamandansa a makon jiya ya ce Abubakar din yana can Mambila cikin tsaunukan jihar Taraba, ko hakan gaskiya ne babu wanda ya tabbatar.

Tana dai iya yiwuwa shashantar da sojoji kwamandan mai suna Abu Muhammad/Abubakar Abdulkadir din yayi, domin rufawa ogansa asiri, tana kuma iya yiwuwa, da gaske yake, ya gaji ne da akidar yake so a kashe musu shugaban domin saura suzo suyi sulhu, kamar yadda ya fada wa manema labarai, cewa Shekau ke hana duk wani shirin sulhu.

Shawara dai yanzu tana hannun soji, ko su farma dajin Sambisa, ko su dumfari na Falgore, ko su nufi Mambila, ko kuma su far ma dukkan yankunan. Fatan mu dai, shine a kawo karshen zub-da jini, ba gaira ba dalili.

‘Wannan rubutu dai ra’ayin edita ne, ba lallai ya zama ra’ayi na HAUSATOP.COM ba.’

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.