Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Wasu Daga Cikin Jarumai Sun Kaiwa Tijjani Asase Agaji

0 1,179

Fitaccen jarumin masana’antar kannywood Tijjani Asase yana mai godiya da nuna farin ciki ga yan’uwa da abokan huldar shi na masana’antar tare da masoyan shi bisa gudummawar da suka bashi kan gidan shi da ya kone.

A daren ranar 3 ga watan febreru ne gidan jarumin ya kone tare da kayayyakin dake cikin ta. Ya sanar cewa babu abun da ya tseratar face iyalen sa domin komai dake cikin gidan ya kone sakamakon gabarar.

Bayan sanarwar da yayi shafin sa na kafafen sada zumunta kan wannan jarabtar da ya abkar masa, jarumai sabbi da tsofaffi tare da jiga-jiga masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood sun ziyarci gidan domin jajenta masa.

Bayan ziyarar da addu’o’in da jarumai suka kai masa, wasu daga cikin su sun agaza masa da kayan abinci da kudi har da sutura.

“Salam barkanmu da safiya da mika godiyata ga iyayan gidana da yayyena wa’yan da suka tayani da alhini. wasu a waya wasu hargida wasa harda gudun mawa sutura da abinci wasu harda kudi nagode Allah yabar zumunci amin nagode”. ya rubuta a shafin sa na instagram.

Game da wannan abun farin ciki da yan’uwa suka yi mashi wannan jarumin ya kasa boye nuna godiya kan ranar da suka nuna mashi. A cewar sa har ma wadanda yake tunanin cewa makiyin shine sun taya shi jaje.

#PulseNG

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.