Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Wata Baturiya tayiwa Wani Dan Najeriya Alkawarin bashi miliyan 145 idan har ya amince zai auri ‘yar ta

0 30

Image result for Ku bani shawara: Baturiya ta yi alkawarin bani miliyan 145 idan har na amince zan auri 'yar taWani dan Najeriya mai suna Johnny Creed yana neman shawarar ‘yan Najeriya bayan da ya ce wata baturiya tayi alkawarin ba shi naira miliyan 145 matukar ya amince zai auri ‘yar ta.

Wani matashin mayaki dan Najeriya mai suna Johnny Creed dan shekara 21 ya bayyana cewar wata baturiya ta amince zata bashi kudi matukar yayi alkawarin auren ‘yar ta mai shekaru 18 a duniya.

Ku bani shawara: Baturiya ta yi alkawarin bani miliyan 145 idan har na amince zan auri 'yar ta

Creed ya ce baturiyar ta furta masa hakan ne bayan da ya fada mata cewar bai taba soyayya da wata ‘ya mace ba. Creed ya kara da cewar Baturiyar ta amince ta ba shi dala dubu 400, kwatankwacin naira miliyan 145 idan har ya yi alkawarin zai auri ‘yarta ta duk da basu taba haduwa da ita ‘yar ba.

Creed dai ya ambata cewar ya shiga cikin rudani tun bayan jin wannan bukata ta baturiya domin yana ganin tamkar wani tarko ne ake so ya fada. A saboda haka ne ya garzayo yake neman shawarar ‘yan Najeriya.

Wacce shawara zaku bawa wannan matashi?

Want To Contact Us For Promotion? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.