Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

Zan maka Buhari Kotu In Yaki Tsayawa Takarar Tazarce A 2019 – Inji Gudaji Kazaure

0 126

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da gidan rediyon BBC Hausa

– ya ce shi tuni har ma ya fadawa shugaban kasar hakan

Fitaccen dan majalisar wakillan nan dake wakiltar mazabar Kazaure, Roni, Gwiwa da kuma ‘Yankwashi watau Honorable Gudaji Kazaure ya sha alwashin sai ya kai Buhari kotu idan har ya kuskura yaki tsayawa takarar tazarce a zaben 2019 mai zuwa.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da gidan rediyon BBC Hausa a satin da ya gabata inda ya bayyana cewa akan shugaba Muhammadu Buhari kam, shi ba gudu ba ja da baya.

NAIJ.com ta samu cewa dan majalisar ya ce shi tuni har ma ya fadawa shugaban kasar hakan a wata haduwa da suka yi a watannin baya inda kuma yace yanzu abunda shugaban yake bukata shine cikakken goyon bayan dukkan al’ummar kasar.

A cewar sa, dole ne sai an sha wuya sannan za’a sha dadi kuma tabbas shugaban kasar ya dauko hanyar gyaran kasar musamman ma yadda ya taras da ita ba kudi amma duk da haka komai na tafiya dai dai.

Want Ur Music/Video On HausaTop? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subcribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.