Home | Music | Videos | Mixtapes | Lyrics | Entertaiment | Kannywood | Instrumentals | News | Biography | Contact

HT ENT: Mawaki Dabo Daprof Yasamu Lambar Girmamawa Na Gwarzon MC A Arewa

0 123

A ranar lahadi biyu ga watan satumba ne, aka karrama shahararren mawakin Hausa Hip Hop, mai Barkwanci, Marubuci, dan film kuma MC da kambun gwarzon MC fitacce a Arewa sakamakon dadewa dakuma kwarewa da yake dashi a fagen MC.

Mawakin ya samu wannan karramawan ne daga kungiyar Real Fans, na shahararren ma’akacin radio a Kano Nura Bello wanda akafi sani da Belnur a yayin bikin cikar kungiyar shekara daya da kafuwa. Taran wanda ya gudana a Darul Tauheed, yasamu halattar manya manya mawaka da baki daban daban.

Kadan daga cikin mawakan sun hadar da
Ali Jita
Bmeri Aboki daga jahar Lagos
AleeGee
Mkay
Abba Fido
mai barkwanci nan yaron mommy daga Lagos
dade sauran su.

Anyi taron cikin farin ciki da tsari mai burgewa, inda Dabo Daprof yayi godiya ga wadan da suka karramashi yakuma sadaukar da kanbun ga masoyan sa.

Want Ur Music/Video On HausaTop? Click Here

Like Us On Facebook
Follow Us On Twitter
Follow Us On Instagram
Subscribe Us On YouTube

Leave A Reply

Your email address will not be published.